Surat An-Nahl, aya ta 115

16:115

إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَيۡتَةَ وَٱلدَّمَ وَلَحۡمَ ٱلۡخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ لِغَيۡرِ ٱللَّهِ بِهِۦۖ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ غَيۡرَ بَاغٖ وَلَا عَادٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ ١١٥

Innamā harrama 'alaykumul-maytata wad-dama walahmal-khinzīri wamā uhilla lighayrillāhi bihī famanidturra ghayra bāghin walā 'ādin fa innallāha ghafūrur rahīm

Abin sani kawai (Allah) Ya haramta1 muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.

Bayanan ƙasa

1 Bayãnin abũbuwan da aka haramta, idan bãbu larũra. Anã cin abin da shari'a ta hana a ci a kan larũra sai idan larũrar ta sãmi mutum ne a cikin hãlin sãɓon Allah, kamar mai fita daga ɗã'ar sarkin Musulunci ya yi tãsa ƙungiya dabam, kõ wanda ya fita dõmin wani zãlunci kamar sãta ga misãli, to, ba su cin haram dõmin su ci gaba da aikinsu.