Surat An-Nahl, aya ta 114

16:114

فَكُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ حَلَٰلٗا طَيِّبٗا وَٱشۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ ١١٤

Fakulū mimmā razaqakumullāhu halālan tayyiban washkurū ni'matallāhi in kuntum iyyāhu ta'budūn

Sa'an nan ku ci daga1 abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai dãɗi, kuma ku gõde wa ni'imar Allah idan kun kasance shi kuke bautãwa.

Bayanan ƙasa

1 Bãyan bayãni a kan hukuncin ridda sabõda sanyãwar sãshen ni'imõmin Allah ga wasu gumãka kõ aljannu kõ waɗansu mutãne sãlihai, sa'an nan Ya yi umurni da cin abin da Allah Ya azurta mutum duka amma da sharuɗɗa uku, watau ya zama halas ga shari'a kuma mai dãɗin ci, wani haƙƙi na wani mutum bai rãtaya ba a kansa ga shari'a, kuma a bi shari'a wajen aikatar da shi kamar yadda Allah Ya ce wajen yanka da mai kama da shi, shi ne gõde wa Allah. Sabõda haka banda kamar giya da kãyan wani mutum sai fa a bisa yardarsa.