Surat Al-Qasas, aya ta 23

28:23

وَلَمَّا وَرَدَ مَآءَ مَدۡيَنَ وَجَدَ عَلَيۡهِ أُمَّةٗ مِّنَ ٱلنَّاسِ يَسۡقُونَ وَوَجَدَ مِن دُونِهِمُ ٱمۡرَأَتَيۡنِ تَذُودَانِۖ قَالَ مَا خَطۡبُكُمَاۖ قَالَتَا لَا نَسۡقِي حَتَّىٰ يُصۡدِرَ ٱلرِّعَآءُۖ وَأَبُونَا شَيۡخٞ كَبِيرٞ ٢٣

Walammā warada mā'a madyana wajada 'alayhi ummatam minan-nāsi yasqūna wawajada min dūnihimumra'atayni tadhūdāni qāla mā khatbukumā qālatā lā nasqī hattā yusdirar-ri'ā'u wa abūnā shaykhun kabīr

Kuma a lõkacin da ya isa mashãyar Madyana, ya sãmi wata jam'ar mutãne sunã shãyarwa, kuma a bãyansu ya sãmi waɗansu mãtã biyu sunã kõrar (tumãkinsu). Ya ce: "Mẽne ne shã'aninku?" Suka ce, "Bã zã mu iya shãyãrwa ba sai makiyãya sun fita, kuma ubanmu tsõho1 ne mai daraja."

Bayanan ƙasa

1 Sabõda girma bã ya zuwa ya shãyar da tumakinsa, sai ya sanya mu, mu 'ya'yansa, kõ da muke mãtã. Wannan ya nũna mace tanã yin aikin maza sabõda larũra. Kuma sabõda darajar ubansu ba su shiga a cikin makiyãya ba dõmin tsaron mutuncinsu don haka ake son asali mai kyau. NĩSantarsu daga maza nau'in ƙauracewa ne na sharĩ'a.