Surat Al-Ma'idah, aya ta 111

5:111

وَإِذۡ أَوۡحَيۡتُ إِلَى ٱلۡحَوَارِيِّـۧنَ أَنۡ ءَامِنُواْ بِي وَبِرَسُولِي قَالُوٓاْ ءَامَنَّا وَٱشۡهَدۡ بِأَنَّنَا مُسۡلِمُونَ ١١١

Wa idh awhaytu ilal-hawāriyyina an āminū bī wabirasūlī qālū āmannā washhad bi annanā muslimūn

"Kuma a lõkacin da Na yi wahayi zuwa ga Hawãriyãwa1 cewa ku yi ĩmãni da Ni, kuma da Manzo Na. Suka ce: "Mun yi ĩmãni, kuma ka shaida da cewa lalle mu, mãsu sallamãwa ne."

Bayanan ƙasa

1 Hawãriyãwa su ne sahabban Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Sunã sanyãwar farãren tufãfi, dõmin haka aka yi musu suna da haka.