Surat Al-Hajj, aya ta 25

22:25

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ ٱلَّذِي جَعَلۡنَٰهُ لِلنَّاسِ سَوَآءً ٱلۡعَٰكِفُ فِيهِ وَٱلۡبَادِۚ وَمَن يُرِدۡ فِيهِ بِإِلۡحَادِۭ بِظُلۡمٖ نُّذِقۡهُ مِنۡ عَذَابٍ أَلِيمٖ ٢٥

Innal-ladhīna kafarū wayasuddūna 'an sabīlillāhi wal-masjidil-harāmil-ladhī ja'alnāhu lin-nāsi sawā'anil-'ākifu fīhi wal-bādi waman yurid fīhi bi ilhādi bizulmin nudhiqhu min 'adhābin alīm

Lalle ne waɗanda suka kãfirta kuma suka taushe (mutãne) daga hanyar Allah da masallaci mai alfarma wanda Muka sanya shi ga mutãne alhãli kuwa mazauni a ciki da baƙauye daidai suke kuma wanda ya yi nufin karkatar1 da gaskiya a cikinsa da zãlunci zã Mu ɗanɗana masa daga wata azãba mai raɗadi.

Bayanan ƙasa

1 Ilhãdi, shĩ ne yin ibãda bã yadda Allah Ya yi umurni da a yi ta ba. Wanda ya yi nufin karkatar da gaskiyar ibãda a cikin hurumin Makka, Allah zai yi masa azãba mai tsanani,balle fa a ce mutum ya aikata. Sabõda haka yanã wajaba ga mai nufin zuwa Hajji ya kõyi yadda ake yin ibãda kãfinya tafi Makka dõmin kada ya jãwo wa kansa halaka.