لِلۡفُقَرَآءِ ٱلَّذِينَ أُحۡصِرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ لَا يَسۡتَطِيعُونَ ضَرۡبٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ يَحۡسَبُهُمُ ٱلۡجَاهِلُ أَغۡنِيَآءَ مِنَ ٱلتَّعَفُّفِ تَعۡرِفُهُم بِسِيمَٰهُمۡ لَا يَسۡـَٔلُونَ ٱلنَّاسَ إِلۡحَافٗاۗ وَمَا تُنفِقُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٌ ٢٧٣
Lil-fuqarā'il-ladhīna uhsirū fī sabīlillāhi lā yastatī'ūna darban fil-ardi yahsabuhumul-jāhilu aghniyā'a minat-ta'affufi ta'rifuhum bisīmāhum lā yas'alūnan-nāsa ilhāfan wamā tunfiqū min khayrin fa innallāha bihī 'alīm
(Ciyarwar a yĩ ta) ga matalautan1 nan waɗanda aka tsare a cikin hanyar Allah, ba su iya tafiyar fatauci a cikin ƙasa, jãhilin hãlinsu yana zaton su wadãtattu sabõda kãmun kai kana sanin su da alãmarsu, ba su rõƙon mutãne da nãcẽwa. Kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, lalle Allah gare shi Masani ne.
Bayanan ƙasa
1 Matalautan nan 'muhãjiruna'ne waɗanda suka bar dũkiyarsu da iyãlansu dõmin hijira. Kuma ba su sãmi wata matãka ba a Madĩna, sai aka yi musu rumfuna, sunã kwãna a ciki, suka tsare kansu dõmin jihãdi da yãƙi da karãtun Alƙur'ãni da ibãda kamar matsayin sõja a yanzu. Sũ wajen ɗari huɗu ne, shugabansu, shi ne Abdur Rahman bn Sakhar Abu Huraira el Dawsy.