Surat Al-Baqarah, aya ta 226

2:226

لِّلَّذِينَ يُؤۡلُونَ مِن نِّسَآئِهِمۡ تَرَبُّصُ أَرۡبَعَةِ أَشۡهُرٖۖ فَإِن فَآءُو فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ ٢٢٦

Llilladhīna yu'lūna min nisā'ihim tarabbusu arba'ati ashhurin fa in fā'ū fa innallāha ghafūrur rahīm

Ga waɗanda suke yin rantsuwa1 daga matansu akwai jinkirin watã huɗu. To, idan sun kõma, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

Bayanan ƙasa

1 Hukuncin ĩlã'i, watau rantsuwa a kan barin tãkin matarsa dõmin ya wahalar da ita, a jira shi wata hudu, idan yã ƙi kõmãwa a sake ta daga gare shi.