Surat Al-Baqarah, aya ta 225

2:225

لَّا يُؤَاخِذُكُمُ ٱللَّهُ بِٱللَّغۡوِ فِيٓ أَيۡمَٰنِكُمۡ وَلَٰكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا كَسَبَتۡ قُلُوبُكُمۡۗ وَٱللَّهُ غَفُورٌ حَلِيمٞ ٢٢٥

Llā yu'ākhidhukumullāhu bil-laghwi fī aymānikum walākin yu'ākhidhukum bimā kasabat qulūbukum wallāhu ghafūrun halīm

Allah ba Ya kãmã ku da laifi sabõda yãsasshiya a cikin rantsuwõyinku. Kuma amma Yana kama ku sabõda abin da zukãtanku1 suka sanã'anta. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.

Bayanan ƙasa

1 Yasasshiyar rantsuwa ita ce, a wurin Mãlik, rantsuwa a kan abin da mutum ke ganin sa tabbatacce ne, sai ya bayyana daga bãya akasin tunãninsa. Kamar ya ce Wallãhi bã ni da kuɗi, ga saninsa kuwa haka ne bã ya da su, bai sani ba ashe wani yã mutu, yã yi gãdo. A Shafi'i ita ce: ã'aha Wallahi, I, wallãhi, a cikin magana bã da nufi ba.