Surat Al-Baqarah, aya ta 224

2:224

وَلَا تَجۡعَلُواْ ٱللَّهَ عُرۡضَةٗ لِّأَيۡمَٰنِكُمۡ أَن تَبَرُّواْ وَتَتَّقُواْ وَتُصۡلِحُواْ بَيۡنَ ٱلنَّاسِۚ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ ٢٢٤

Walā taj'alullāha 'urdatal li aymānikum an tabarrū watattaqū watuslihū baynan-nāsi wallāhu samī'un 'alīm

Kuma kada ku sanya1 Allah kambu ga rantsuwõyinku dõmin kada ku yi wani alhẽri, kuma ku yi taƙawa, kuma ku yi wani gyara tsakãnin mutãne, kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.

Bayanan ƙasa

1 Bãyanin rantsuwa da hukunce-hukuncenta. Kada ku sanya rantsuwa da Allah sababin rashin aikata wani alheri, kõ wani aikin ɗã'a, kõ kuma sanya sulhu a tsakanin mutãne, kamar a rõƙe shi ga wani abu daga cikinsu, sai ya yi rantsuwa ya ce: "Wallãhi bã zan yi ba," dõmin tsare kansa daga aikatãwar abin da aka nema gare shi. Yin irin wannan rantsuwa makarũhi ne kõ haram, gwargwadon nauyin abin da aka yi ta sabõda rashin yin sa. Kambu shi ne wurin gwada harbi.