Surat Al-An'am, aya ta 121

6:121

وَلَا تَأۡكُلُواْ مِمَّا لَمۡ يُذۡكَرِ ٱسۡمُ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ وَإِنَّهُۥ لَفِسۡقٞۗ وَإِنَّ ٱلشَّيَٰطِينَ لَيُوحُونَ إِلَىٰٓ أَوۡلِيَآئِهِمۡ لِيُجَٰدِلُوكُمۡۖ وَإِنۡ أَطَعۡتُمُوهُمۡ إِنَّكُمۡ لَمُشۡرِكُونَ ١٢١

Walā ta'kulū mimmā lam yudhkarismullāhi 'alayhi wa innahū lafisqun wa innash-shayātīna layūhūna ilā awliyā'ihim liyujādilūkum wa in ata'tumūhum innakum lamushrikūn

Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sũnan Allah ba a kansa.1 Kuma lalle ne shĩ fãsiƙanci ne. Kuma lalle ne, shaiɗãnu, haƙĩƙa, suna yin ishãra zuwa ga masõyansu, dõmin su yi jãyayya da ku. Kuma idan kuka yi musu ɗã'a, lalle ne kũ, haƙĩƙa, mãsu shirki ne.

Bayanan ƙasa

1 Sabõda haka bã a cin yankan majũsu. Anã cin yankan bakitãbe, babu ruwanmu da abin da yake faɗa, tun da Allah Ya halatta mana cin abincinsu alhãli kuwa Ya san sun riga sun musanya addininsu. Idan Musulmi ya bar sũnan Allah da gangan, amma bai ambaci sũnan kõwa ba, to, akwai riwãya biyu game da haka, ci kõ rashin ci. Amma idan ya haɗa sũnan Allah da na wani, to, ba zã a ci ba, dõmin yã yi ridda.