Rabbana hab lana min azwajina

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

وَٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا هَبۡ لَنَا مِنۡ أَزۡوَٰجِنَا وَذُرِّيَّٰتِنَا قُرَّةَ أَعۡيُنٖ وَٱجۡعَلۡنَا لِلۡمُتَّقِينَ إِمَامًا ٧٤

Walladhīna yaqūlūna rabbanā hab lanā min azwājinā wadhurriyyātinā qurrata a'yunin waj'alnā lil-muttaqīna imāmā

Kuma waɗanda suke cẽwa "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya1 mu shũgabanni ga mãsu taƙawa."

Bayanan ƙasa

1 Anã son mutum ya rõƙi Allah Ya ɗaukaka shi, shi da zuriyarsa, ɗaukakar addini, kamar yadda Annabi Ibrãhĩm ya yi rõƙon haka. Kuma wannan yanã cikin sifõfin Bãyin Mai rahama.

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Karanta Surat Al-Furqan gaba ɗaya

Tambayoyi

Ina Rabbana hab lana min azwajina take a cikin Alƙur'ani?

Rabbana hab lana min azwajina tana cikin Surat Al-Furqan, 25:74.