La ikraha fid-din

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

لَآ إِكۡرَاهَ فِي ٱلدِّينِۖ قَد تَّبَيَّنَ ٱلرُّشۡدُ مِنَ ٱلۡغَيِّۚ فَمَن يَكۡفُرۡ بِٱلطَّٰغُوتِ وَيُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱسۡتَمۡسَكَ بِٱلۡعُرۡوَةِ ٱلۡوُثۡقَىٰ لَا ٱنفِصَامَ لَهَاۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ ٢٥٦

Lā ikrāha fid-dīni qat tabayyanar-rushdu minal-ghayyi faman yakfur bit-tāghūti wayu'mim billāhi faqadistamsaka bil-'urwatil-wuthqā lanfisāma lahā wallāhu samī'un 'alīm

Bãbu tĩlastãwa1 a cikin addini, haƙĩƙa shiriya tã bayyana daga ɓata; Sabõda haka wanda ya kãfirta da ¦ãgũta kuma ya yi ĩmãni da Allah, to, haƙĩƙa, yã yi riƙo ga igiya amintacciya, bãbu yankẽwa agare ta. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.

Bayanan ƙasa

1 Abũbuwan bautãwa, iri biyu ne; Ubangijin da Yã aiko Muhammadu da wannan gaskiya da shiriya Shĩ ne Allah, da sauran iyãyen giji mãsu dõkõkin kai da na son zũkãta kamar nafsu da Shaiɗan, na aljannu da mutãne, mãsu ƙãga abin da suke so, su ƙira mutane a kansa ana ce musu Ɗãgũtu. Ya yi bayãnin sakamakon mabiyin kõwane irin bautawar. Sa'an nan ya biyar da ƙissõshi uku dõmin bayãnin abin da wannan magana ta ƙunsa; ta farko Namarũzu tãre da Ibrãhĩm, tanã nũna cewa mai mulki anã umurtar sa da bin Allah da taƙawa, idan ya bi son zũciyarsa, to, ya zama Ɗãgũtu. Allah zai halakar da shi. Ta biyu ƙissar Uzairu, tanã nũna cewa bãbu abin da yake da wuya ga Allah. Ta uku ƙissar Ibrãhim da yadda Allah ke rãyar da matattu, tanã nũna cewa bãbu laifi ka roƙi Allah Ya gãnar da kai dukan abin da ya shige maka duhu dõmin ka ƙãrã ĩmãni.

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Karanta Surat Al-Baqarah gaba ɗaya

Tambayoyi

Ina La ikraha fid-din take a cikin Alƙur'ani?

La ikraha fid-din tana cikin Surat Al-Baqarah, 2:256.