ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ عَلَىٰ عَبۡدِهِ ٱلۡكِتَٰبَ وَلَمۡ يَجۡعَل لَّهُۥ عِوَجَاۜ ١
Al-hamdu lillāhil-ladhī anzala 'alā 'abdihil-kitāba walam yaj'al lahū 'iwajā
Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya saukar da Littafi a kan bãwansa kuma bai sanya karkata ba a gare shi.
قَيِّمٗا لِّيُنذِرَ بَأۡسٗا شَدِيدٗا مِّن لَّدُنۡهُ وَيُبَشِّرَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ أَجۡرًا حَسَنٗا ٢
Qayyimal liyundhira ba san shadīdam mil ladunhu wayubasshiral-mu'minīnal-ladhīna ya'malūnas-sālihāti anna lahum ajran hasanā
Madaidaici, dõmin Ya yi gargaɗi da azãba mai tsanani daga gare shi, kuma Ya yi bushãra ga mũminai, waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai da (cẽwa) sunã da wata lãdã mai kyau.
مَّٰكِثِينَ فِيهِ أَبَدٗا ٣
Mmākithīna fīhi abadā
Sunã mãsu zama a cikinta har abada.
وَيُنذِرَ ٱلَّذِينَ قَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدٗا ٤
Wayundhiral-ladhīna qālut-takhadhallāhu waladā
Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda1 suka ce: "Allah yanã da ɗa."
Bayanan ƙasa
1 Lãrabawa sun ce malã'iku 'ya'yan Allah ne. Yahũdawa sunce Uzairu ɗan Allah ne, Nasãra sun ce Ĩsã ɗan Allah ne. Bãbu ladabi ga faɗin wannan magana. Sabõda haka Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya gaya musu, cewa wannan magana ƙarya ce kuma rashin ladabi ne ga Allah, da ba su yi ĩmãni ba, ya ji tsõro kada ya zama shĩ ne ya yi ƙwauron bãki ga faɗã musu gaskiya. Sai Allah Ya gaya masa, cewa kada ya halakar da ransa dõmin baƙin cikin haka.
مَّا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٖ وَلَا لِأٓبَآئِهِمۡۚ كَبُرَتۡ كَلِمَةٗ تَخۡرُجُ مِنۡ أَفۡوَٰهِهِمۡۚ إِن يَقُولُونَ إِلَّا كَذِبٗا ٥
Mmā lahum bihī min 'ilmin walā li'ābā'ihim kaburat kalimatan takhruju min afwāhihim in yaqūlūna illā kadhibā
Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyãyensu bã su da shi, abin da ke fita daga bãkunansu ya girma ga ya zama kalmar faɗa! Ba su faɗan kõme fãce ƙarya.
فَلَعَلَّكَ بَٰخِعٞ نَّفۡسَكَ عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِمۡ إِن لَّمۡ يُؤۡمِنُواْ بِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ أَسَفًا ٦
Fala'allaka bākhi'un nafsaka 'alā āthārihim il lam yu'minū bihādhal-hadīthi asafā
To, kã yi kusa ka halaka ranka a gurabbansu, wai dõmin ba su yi ĩmãni da wannan lãbãri ba sabõda baƙin ciki.
إِنَّا جَعَلۡنَا مَا عَلَى ٱلۡأَرۡضِ زِينَةٗ لَّهَا لِنَبۡلُوَهُمۡ أَيُّهُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗا ٧
Innā ja'alnā mā 'alal-ardi zīnatal lahā linabluwahum ayyuhum ahsanu 'amalā
Lalle ne Mũ, Mun sanya abin da ke kan ƙasa wata ƙawa1 ce gare ta, dõmin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau ga aiki.
Bayanan ƙasa
1 Sabõda haka ƙawar ƙasa, kamar furen itãcenta ne, bã su ruɗin mai hankali ga tsarewar ladabi tãre da Ubangijinsa, da bin sharĩ'ar Littafin da aka saukar wa Annabi kuma ba a sanya masa karkata ba.
وَإِنَّا لَجَٰعِلُونَ مَا عَلَيۡهَا صَعِيدٗا جُرُزًا ٨
Wa innā lajā'ilūna mā 'alayhā sa'īdan juruzā
Kuma lalle Mũ, Mãsu sanya abin da ke a kanta (ya zama) turɓãya ƙeƙasasshiya ne.
أَمۡ حَسِبۡتَ أَنَّ أَصۡحَٰبَ ٱلۡكَهۡفِ وَٱلرَّقِيمِ كَانُواْ مِنۡ ءَايَٰتِنَا عَجَبًا ٩
Am hasibta anna ashābal-kahfi war-raqīmi kānū min āyātinā 'ajabā
Ko kuwa kã yi zaton cẽwa ma'abũta kõgo1 da allo sun kasance abin mãmãki daga ãyõyin Allah?
Bayanan ƙasa
1 Lõkacin da Allah Ya ce: "kada Annabi ya wahalar da kansa dõmin baƙin cikin ba a karɓi maganarsa ba, sai Ya ba shi lãbãrin ma'abũta kõgo, yadda suka yi gudun hijira da addininsu, Allah Ya tsare su daga wahala, a cikin halin abin al'ajabi. Sa'an nan ƙissar ta tattara a kan ladubba waɗanda ake nħman Mutum ya tsare su tãre da Ubangijinsa a cikin dukan mõtsinsa, kamar yadda bayãni zai nũna.
إِذۡ أَوَى ٱلۡفِتۡيَةُ إِلَى ٱلۡكَهۡفِ فَقَالُواْ رَبَّنَآ ءَاتِنَا مِن لَّدُنكَ رَحۡمَةٗ وَهَيِّئۡ لَنَا مِنۡ أَمۡرِنَا رَشَدٗا ١٠
Idh awal-fityatu ilal-kahfi faqālū rabbanā ātinā mil ladunka rahmatan wahayyi' lanā min amrinā rashadā
A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: "Ya Ubangijinmu1! Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (sãmun) shiriya daga al'amarinmu."
Bayanan ƙasa
1 Sun fara da addu'a ta nħman shiriya daga Allah, Ubangijinsu. Addu'a tun farko ga kõme ladabi ne. Kuma fãrãwa da nũna bautarsu ga Ubangiji, ladabi ne. Hijira da addini 1adabi ne, kuma amincewa da sãmun rahamar Allah, ladabi ne ga Allah, sabõda haka Allah ya jiɓinci tsaron kõgon ya zame musu mafi kyawun wurin zama.
Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.