La ilaha illa anta subhanaka

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

وَذَا ٱلنُّونِ إِذ ذَّهَبَ مُغَٰضِبٗا فَظَنَّ أَن لَّن نَّقۡدِرَ عَلَيۡهِ فَنَادَىٰ فِي ٱلظُّلُمَٰتِ أَن لَّآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنتَ سُبۡحَٰنَكَ إِنِّي كُنتُ مِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ ٨٧

Wadhan-nūni id dhahaba mughādiban fazanna al lan naqdira 'alayhi fanādā fiz-zulumāti al lā ilāha illā anta subhānaka innī kuntu minaz-zālimīn

Kuma mai kifi1 a sã'ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cẽwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cẽwa, "Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai."

Bayanan ƙasa

1 Shĩ ne Yũnus bn Matta. Yãyi hushi da mutãnensa dõmin ba su karɓi addini ba, sai ya bar su tun a gabãnin a yi masa iznin barinsu. Sai Allah Ya jarrabe shi da fãɗãwã cikin ruwa har wani kĩfi ya haɗiye Shi, sa'an nan kuma ya amãyo Shi a bãyan wahala, ya kõma wa mutãnensa. Suka yĩ ĩmãni.

فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ وَنَجَّيۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡغَمِّۚ وَكَذَٰلِكَ نُـۨجِي ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٨٨

Fastajabnā lahū wanajjaynāhu minal-ghammi wakadhālika nujil-mu'minīn

Sai Muka karɓa masa kuma Muka tsĩrar da shi daga baƙin ciki. Kamar haka ne Muke tsĩrarda masu ĩmãni.

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Karanta Surat Al-Anbiya gaba ɗaya

Tambayoyi

Ina La ilaha illa anta subhanaka take a cikin Alƙur'ani?

La ilaha illa anta subhanaka tana cikin Surat Al-Anbiya, 21:87-88.