إِنَّ ٱللَّهَ لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۚ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٖ ١١٦
Innallāha lahū mulkus-samāwāti wal-ardi yuhyī wayumītu wamā lakum min dūnillāhi min waliyyin walā nasīr
Lalle ne Allah Yanã1 da mulkin sammai da ƙasa, Yanã rãyarwa kuma Yanã matarwa. Kuma bã ku da wani masõyi, kuma bã ku da mataimaki, baicin Allah.
Bayanan ƙasa
1 Wannan ãyã tanã nũna cewa taklĩfin da Allah Yake azã wa bãyinSa na yãƙi da waninSa, bã dõmin ya wahalar da su ba ne. Yanã yi ne dõmin alheri a gare su, Shĩ Allah Mawãdaci ne, Yanã da ƙasa da sammai, kuma shĩ ne Mai yin halittar kõme.