Surat At-Tawbah, aya ta 106

9:106

وَءَاخَرُونَ مُرۡجَوۡنَ لِأَمۡرِ ٱللَّهِ إِمَّا يُعَذِّبُهُمۡ وَإِمَّا يَتُوبُ عَلَيۡهِمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ ١٠٦

Wa ākharūna murjawna li amrillāhi immā yu'addhibuhum wa immā yatūbu 'alayhim wallāhu 'alīmun hakīm

Kuma da waɗansu waɗanda1 aka jinkirtar ga umurnin Allah, kõ dai Ya yi musu azãba kõ kuma Ya karɓi tũba a kansu. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.

Bayanan ƙasa

1 Wata ƙungiya wadda ita ba munãfuka ba ce, amma kuma ba su fita zuwa yãƙin ba, kuma bã su da wani dalĩli sai kasãla kawai da taushewar Shaiɗan. Waɗannan an jinkirtar da al'amarinsu har Allah Ya yi hukunci a kansu.