Surat Ash-Shu'ara, aya ta 3

26:3

لَعَلَّكَ بَٰخِعٞ نَّفۡسَكَ أَلَّا يَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ ٣

La'allaka bākhi'un nafsaka allā yakūnū mu'minīn

Tsammãninka kai mai zaka halakar da ranka ne, dõn ba su zamanto mũminai ba! 1

Bayanan ƙasa

1 Wannan yã nũna cewa Annabi Muhammadu yanã jin tsõron rashin ĩmãnin mutãnensa, kada ya zama shĩ ne ya gajarta daga abin da Allah Ya ɗõra a kansa, na iyar da manzanci. Haka mũmini yake, kullum girman Ubangijinsa yake dũbi, sabõda haka kõme ya yi na ɗã'a, sai ya ga kãsãwar kansa ga tsayuwa da hakkin Ubangijinsa, a kansa, ya ƙãra jin tsõro da tawãli'u.