فَٱلزَّٰجِرَٰتِ زَجۡرٗا ٢
Faz-zājirāti zajrā
Sa'an nan mãsu yin tsãwa1 dõmin gargaɗi.
Bayanan ƙasa
1 Mãsu tsãwa, sũ ne Malamai mãsu sãmun ilmin wa'azi daga Annabãwa waɗanda ke karãtun abin tunãwa daga Allah Ubangijin sammai da ƙasa, Mai bãyar da haske ga rãnã, Mai haskaka taurari mãsu ƙãwãtar da samã kuma su tsare ta daga shaiɗanu. An siffanta rãnã da Annabãwa, Malamai da taurãri, ilmi da haske da sababin ƙawa da shiryarwa da kõrar mãsu ɓarna.