Surat An-Nisa, aya ta 69

4:69

وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ فَأُوْلَٰٓئِكَ مَعَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ وَٱلصِّدِّيقِينَ وَٱلشُّهَدَآءِ وَٱلصَّٰلِحِينَۚ وَحَسُنَ أُوْلَٰٓئِكَ رَفِيقٗا ٦٩

Waman yuti'illāha war-rasūla fa ulā'ika ma'al-ladhīna an'amallāhu 'alayhim minan-nabiyyina was-siddīqīna wash-shuhadā'i was-sālihīna wahasuna ulā'ika rafīqā

Kuma waɗannan da suka yi ɗã'a ga Allah da Mazonsa, to, waɗannan sunã tãre da waɗanda Allah Ya yi ni'ima a kansu, daga annabãwa da mãsu yawan gaskatãwa, da masu shahãda1 da sãlihai. kuma waɗannan sun kyautatu ga zama abõkan tafiya.

Bayanan ƙasa

1 Darajar ɗaukaka ga addini shi ne zama Annabi sa'an nan siddĩƙ, watau manyan sahabban kowane Annabi. Waɗannan darajõji biyu yanzu an rufe su daga kõwa, dõmin bãbu sauran Annabci wanda yake tãre da siddĩƙanci. Ta uku ita ce shahãda watau a kashe mutum a wurin yãƙi dõmin ɗaukaka kalmar Allah da tsare haƙƙõƙin Musulmi. Wannan ita ce maƙasudin abin faɗa a nan, dõmin abin da sũrar ke karantarwa, kuma dõmin ya zama shimfiɗar magana a kan darajar jihãdi da amfanõninsa. Ta huɗu zama sãlihi mai son abin da Allah Yake so kuma mai ƙin abin da Allah Yake ƙi.