Surat Al-Kahf, aya ta 42

18:42

وَأُحِيطَ بِثَمَرِهِۦ فَأَصۡبَحَ يُقَلِّبُ كَفَّيۡهِ عَلَىٰ مَآ أَنفَقَ فِيهَا وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَيَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي لَمۡ أُشۡرِكۡ بِرَبِّيٓ أَحَدٗا ٤٢

Wa uhīta bithamarihī fa asbaha yuqallibu kaffayhi 'alā mā anfaqa fīhā wahiya khāwiyatun 'alā 'urūshihā wayaqūlu yālaytanī lam ushrik birabbī ahadā

Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itãcensa, sai ya wãyi gari yanã jũyar da tãfunansa biyu, sabõda abin da ya kashe a cikinta, alhãli kuwa ita tanã kwance a kan rassanta, kuma yanã cẽwa, "Kaitõna, dã dai ban tãra1 wani da Ubangijina ba!"

Bayanan ƙasa

1 Ya yi nadãmar halakar gõnar kawai, amma bai yi nadãmar kãfircin shirkin da ya yi ba, sabõda haka Allah bai mayar masa da badalinta ba. Daga nan kuma anã fahimtar cewa rashin mai da al'amari ga Allah shirku ne, kuma girman kai sabõda dũkiya, shirku ne wanda ƙawar dũniya ke sanya wãwãye a ciki.