وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ قَالَ ءَأَسۡجُدُ لِمَنۡ خَلَقۡتَ طِينٗا ٦١
Wa idh qulnā lil-malā'ikatisjudū li'ādama fasajadū illā iblīsa qāla a'asjudu liman khalaqta tīnā
Kuma a lõkacin1 da Muka cẽ wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu," sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa, ya ce: "shin, zan yi sujada ga wanda ka2 halitta shi yanã lãka?"
Bayanan ƙasa
1 Muƙãrana a tsakãnin jinsin mutum da malã'iku da aljannu. An fĩfĩtar da jinsin mutum da sanya wa sauran jinsõshi biyu su yi masa sujada, sa'an nan aka ɗaukaka jinsin malã'ika sabõda ɗã'a, kuma aka la'anci jinsin Iblĩsa da sãɓo.
2 Rubũta "ka" da ƙaramin "ka" ne kõ da yake lamĩrin Allah ne, dõmin ya nuna hãlin maganar Shaiɗan zuwa ga Allah Mai girma. Yanã yin maganar da hushi, ba da girmamawa ba.