Surat Al-Baqarah, aya ta 284

2:284

لِّلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَإِن تُبۡدُواْ مَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ أَوۡ تُخۡفُوهُ يُحَاسِبۡكُم بِهِ ٱللَّهُۖ فَيَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ ٢٨٤

Lillāhi mā fis-samāwāti wamā fil-ardi wa in tubdū mā fī anfusikum aw tukhfūhu yuhāsibkum bihillāhu fayaghfiru liman yashā'u wayu'addhibu man yashā'u wallāhu 'alā kulli shay'in qadīr

Allah ne, da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma idan kun bayyana abin da yake a cikin zukatanku (na shaida), ko kuka ɓõye shi, Allah zai bincike ku da shi, sa'an nan Ya yi gãfara ga wanda Yake so, kuma Ya azabta wanda Yake so. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.1

Bayanan ƙasa

1 Wannan ãyã ita ce ƙarshen bayãni a kan bãyar da shaida. A kan shaidar da mutum ya bayyana kõ ya ɓõye a cikin rai, Allah Yake yi masa bincike dõmin hakkin wani da ya rãtaya a kan wannan bayyanawar kõ ɓõyewar. Ita ayar da biyu na bayanta sun ƙunshi ilmin Baƙara dukanta.