وَقَالَ لَهُمۡ نَبِيُّهُمۡ إِنَّ ٱللَّهَ قَدۡ بَعَثَ لَكُمۡ طَالُوتَ مَلِكٗاۚ قَالُوٓاْ أَنَّىٰ يَكُونُ لَهُ ٱلۡمُلۡكُ عَلَيۡنَا وَنَحۡنُ أَحَقُّ بِٱلۡمُلۡكِ مِنۡهُ وَلَمۡ يُؤۡتَ سَعَةٗ مِّنَ ٱلۡمَالِۚ قَالَ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰهُ عَلَيۡكُمۡ وَزَادَهُۥ بَسۡطَةٗ فِي ٱلۡعِلۡمِ وَٱلۡجِسۡمِۖ وَٱللَّهُ يُؤۡتِي مُلۡكَهُۥ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ ٢٤٧
Waqāla lahum nabiyyuhum innallāha qad ba'atha lakum tālūta malikan qālū annā yakūnu lahul-mulku 'alaynā wanahnu ahaqqu bil-mulki minhu walam yu'ta sa'atam minal-māli qāla innallāhastafāhu 'alaykum wazādahū bastatan fil-'ilmi wal-jismi wallāhu yu'tī mulkahū man yashā'u wallāhu wāsi'un 'alīm
Kuma annabinsu1 ya ce musu: "Lalle ne, Allah ya naɗa muku ¦ãlũta2 ya zama sarki." Suka ce: "Yãya ne sarauta zã ta kasance a gare shi, a kanmu, alhãli kuwa mũ ne mafi cancanta da sarauta daga gare shi, kuma ba a bã shi wata wadata ba daga dũkiya?" Ya ce: "Lalle ne, Allah Yã zãɓe shi a kanku, kuma Ya ƙãra masa yalwa a cikin ilmi da jiki. Kuma Allah Yana bãyar da mulkinSa ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadaci ne, Masani.
Bayanan ƙasa
1 Sũnan Annabinsu Shamwĩlu daga Sibt Lãwaya. A bãyan Mũsã Yũsha'u bin Nũn sa'an nan Kãlib, sa'an nan Hizƙĩl, sa'an nan Ilyas sa'an nan Alyasa'u, daga nan Bani Isrã'ila suka rasa mai jan su har Amãliƙa ɗiyan Amlĩƙ bn Ãd waɗanda ke zaune a Falastĩn suka rinjãyi Bani Isrã'ila, suka karkashe su suka kõre su daga gidãjensu suka kãma 'ya'yansu, har a lõkacin da wata mace daga Sibt Lãwaya ta haifi Shamwĩlu Annabi. Ya naɗa musu sarki Ɗãlũta.
2 Ɗãlũta yana a cikin gidan Binyãminu ɗan Ya'aƙũbu talakãwa ne sunã dõgara a kan sanã'a. Zũriyyar Yahũza, sũ ne sarãkuna dõmin haka sunansu ya rinjãya a kan Bani Isra'ila. Zũriyyar Lãwaya sũ ne Annabãwa da mãlamai.