Surat Al-Baqarah, aya ta 246

2:246

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلۡمَلَإِ مِنۢ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ مِنۢ بَعۡدِ مُوسَىٰٓ إِذۡ قَالُواْ لِنَبِيّٖ لَّهُمُ ٱبۡعَثۡ لَنَا مَلِكٗا نُّقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ قَالَ هَلۡ عَسَيۡتُمۡ إِن كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِتَالُ أَلَّا تُقَٰتِلُواْۖ قَالُواْ وَمَا لَنَآ أَلَّا نُقَٰتِلَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَقَدۡ أُخۡرِجۡنَا مِن دِيَٰرِنَا وَأَبۡنَآئِنَاۖ فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقِتَالُ تَوَلَّوۡاْ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلظَّٰلِمِينَ ٢٤٦

Alam tara ilal-mala'i mim banī isrā'īla mim ba'di mūsā idh qālū linabiyyil lahumub'ath lanā malikan nuqātil fī sabīlillāhi qāla hal 'asaytum in kutiba 'alaykumul-qitālu allā tuqātilū qālū wamā lanā allā nuqātila fī sabīlillāhi waqad ukhrijnā min diyārinā wa abnā'inā falammā kutiba 'alayhimul-qitālu tawallaw illā qalīlam minhum wallāhu 'alīmu biz-zālimīn

Shin, ba ka gani ba zuwa ga wasu mashãwarta1 daga Bani Isrã'ĩla daga bãyan Mũsã, a lõkacinda suka ce ga wani annabi nãsu: "Naɗã mana sarki, mu yi yãƙi a cikin hanyar Allah." Ya ce: "Ashe, akwai tsammãninku idan an wajabta yãƙi a kanku cẽwa bã zã ku yi yãƙin ba?" Suka ce: "Kuma mẽne ne a gare mu, ba zã mu yi yãƙi ba, a cikin hanyar Allah, alhãli kuwa, haƙiƙa, an fitar da mu daga gidãjenmu da ɗiyanmu?" To, a lõkacin da aka wajabta yãƙin a kansu, suka jũya, sai kaɗan daga gare su. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai.

Bayanan ƙasa

1 Wannan ƙissa tana nũna cewa ba a iya yin yãƙi sai da sarki' shũgaba. Kuma ta fadi dalĩlin da ke sanya jama'a su yi yãƙi; watau dõmin tsaron addini da rãyuka da nasaba da mutunci da dũkiya.