Surat Al-Baqarah, aya ta 113

2:113

وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ لَيۡسَتِ ٱلنَّصَٰرَىٰ عَلَىٰ شَيۡءٖ وَقَالَتِ ٱلنَّصَٰرَىٰ لَيۡسَتِ ٱلۡيَهُودُ عَلَىٰ شَيۡءٖ وَهُمۡ يَتۡلُونَ ٱلۡكِتَٰبَۗ كَذَٰلِكَ قَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَ مِثۡلَ قَوۡلِهِمۡۚ فَٱللَّهُ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ ١١٣

Waqālatil-yahūdu laysatin-nasārā 'alā shay'in waqālatin-nasārā laysatil-yahūdu 'alā shay'in wahum yatlūnal-kitāba kadhālika qālal-ladhīna lā ya'lamūna mithla qawlihim fallāhu yahkumu baynahum yawmal-qiyāmati fīmā kānū fīhi yakhtalifūn

Kuma Yahũdãwa suka ce: "Nasãra ba su zamana a kan kõme ba,"1 kuma Nasãra suka ce: "Yahũdãwa ba su zamana a kan kõmeba," alhãli kuwa su, suna karãtun Littãfi. Kamar wancan ne waɗanda ba su sani ba suka faɗa, kamar maganarsu sabõda haka Allah ne ke yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma, a cikin abin da suka kasance suna sãɓawa jũna a cikinsa.

Bayanan ƙasa

1 Mai gaskiya idan marasa gaskiya sun tãru sunã faɗa da shi, to, rashin jituwar tsakãninsu zai sanya Allah Ya kange shi daga sharrinsu, sũ duka, kamar husumar da ke tsakãnin Yahũdu da Nasãra da kuma tsakãnin sũ mushirikai, su duka mãsu yãƙi da Musulmi ne kuma mãsu sãɓãwa jũnã ne wajen aƙidõjinsu.