Surat Al-Anfal, aya ta 12

8:12

إِذۡ يُوحِي رَبُّكَ إِلَى ٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ أَنِّي مَعَكُمۡ فَثَبِّتُواْ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۚ سَأُلۡقِي فِي قُلُوبِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلرُّعۡبَ فَٱضۡرِبُواْ فَوۡقَ ٱلۡأَعۡنَاقِ وَٱضۡرِبُواْ مِنۡهُمۡ كُلَّ بَنَانٖ ١٢

Idh yūhī rabbuka ilal-malā'ikati annī ma'akum fathabbitul-ladhīna āmanū sa'ulqī fī qulūbil-ladhīna kafarur-ru'ba fadribū fawqal-a'nāqi wadribū minhum kulla banān

A lõkacin da Ubangijinka Yake yin wahayi zuwa ga Malã'iku cẽwa: "Lalle ne Ni, Inã tãre da ku, sai ku tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni: Zã Ni jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta, sai ku yi dũka bisa ga wuyõyi kuma ku yi dũka daga gare su ga dukkan yãtsu.1

Bayanan ƙasa

1 Sa'an nan kuma Annabi da umurnin Allah ya ɗebi tsakuwa da hannunsa mai daraja ya jefa a jihar kãfirai. Bãbu wanda ya rage a cikinsu, fãce tsakuwar nan tã shiga a cikin idãnunsa.