وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوّٗا شَيَٰطِينَ ٱلۡإِنسِ وَٱلۡجِنِّ يُوحِي بَعۡضُهُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٖ زُخۡرُفَ ٱلۡقَوۡلِ غُرُورٗاۚ وَلَوۡ شَآءَ رَبُّكَ مَا فَعَلُوهُۖ فَذَرۡهُمۡ وَمَا يَفۡتَرُونَ ١١٢
Wakadhālika ja'alnā likulli nabiyyin 'aduwwan shayātīnal-insi wal-jinni yūhī ba'duhum ilā ba'din zukhrufal-qawli ghurūran walaw shā'a rabbuka mā fa'alūhu fadharhum wamā yaftarūn
Kuma kamar wancan ne Muka sanya wa kõwane Annabi maƙiyi; shaiɗãnun mutãne da aljannu, sãshensu yanã yin ishãra1 zuwa sãshe da ƙawãtaccen zance bisa ga rũɗi. Kuma dã Ubangijinka Yã so, dã ba su aikatã shi ba, don haka ka bar su da abin da, suke ƙirƙirãwa.
Bayanan ƙasa
1 Wahayin shaiɗãnu sãshensu zuwa ga sãshe da ƙãwata ƙarya ta zama kamar gaskiya. Kamar Shaiɗan ya sanya wasiwãsi: Dã da'awar Annabi gaskiya ce: Ai dã manyan mutãne ne zã su fãra bin ta, ba matalautã ba, kõ kuwa annabi mai sihiri ne dõmin yanã raba miji da mãta, da ɗa da uba. Watau su karkatar da magana, dõmin su karkatar da wãwãye daga bin gaskiya.