۞ لَّقَدۡ كَانَ فِي يُوسُفَ وَإِخۡوَتِهِۦٓ ءَايَٰتٞ لِّلسَّآئِلِينَ ٧
Llaqad kāna fī yūsufa wa ikhwatihī āyātul lis-sā'ilīn
Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi1 sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa2 dõmin mãsu tambaya.
Bayanan ƙasa
1 Ãyõyi a nan, anã nufin hãlãye waɗanda suka zama darussa na kõyarwa ga mutãne dõmin tarbiyya ga yãra da manya na kõwane matsayi ga rãyuwar ɗan Ãdam.
2 Yũsufu da ɗan'uwansa shaƙĩƙi, Binyãmĩnu, da sauran gõma. Babbansu ga shekaru, shi ne Raubĩlu, kuma sai Lãwiya. A cikin gidansa aka yi Annabãwa, sai Yahũza kuma shĩ ne shũgabansu a ra'ayi, shĩ ne uban sarãkunansu, sabõda haka sũnansa ya rinjãya a kan ƙabĩlar, aka ce musu Yahũdu.