۞ وَقَالَ نِسۡوَةٞ فِي ٱلۡمَدِينَةِ ٱمۡرَأَتُ ٱلۡعَزِيزِ تُرَٰوِدُ فَتَىٰهَا عَن نَّفۡسِهِۦۖ قَدۡ شَغَفَهَا حُبًّاۖ إِنَّا لَنَرَىٰهَا فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ ٣٠
Waqāla niswatun fil-madīnatimra'atul-'azīzi turāwidu fatāhā 'an nafsihī qad shaghafahā hubban innā lanarāhā fī dalālim mubīn
Kuma waɗansu mãtã1 a cikin Birnin suka ce: "Matar Azĩz tanã nẽman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin taa cikin ɓata bayyanãnna."
Bayanan ƙasa
1 Tsegumin mãtã a cikin gari da yadda mãtar Azĩz ta yi maganin tsegumin, ta hanyar yiwa mãtan liyafa. Mace bã ta kunyar mãtã 'yan'uwanta ga irin wannan fitina idan ta sãme ta, ita kaɗai, balle mãtã ga sũ duka sun kãmu a cikin tarkon da ya kãma ta. Sai ta gaya musu gaskiyar abin da ya auku a tsakãninta da Yũsufu, a bãyan ta rãma zargin da suka yi mata.