Surat Yusuf, aya ta 26

12:26

قَالَ هِيَ رَٰوَدَتۡنِي عَن نَّفۡسِيۚ وَشَهِدَ شَاهِدٞ مِّنۡ أَهۡلِهَآ إِن كَانَ قَمِيصُهُۥ قُدَّ مِن قُبُلٖ فَصَدَقَتۡ وَهُوَ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ ٢٦

Qāla hiya rāwadatnī 'an nafsī washahida shāhidum min ahlihā in kāna qamīsuhū qudda min qubulin fasadaqat wahuwa minal-kādhibīn

Ya ce: "Ita ce ta nẽme ni a kaina."Kuma wani mai shaida daga mutãnenta ya bãyar da shaida: 1"Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tã yi gaskiya, kuma shĩ ne daga maƙaryata."

Bayanan ƙasa

1 Bãyar da shaida a kan al'ãda, mai bãyar da shaidar yanã gabãtar da ita da magana a kan Yusufu, dõmin a ganinsa tuhuma a kanta, tã fi karfi, kuma zumuntarsa da ita ba ta ɗauke shi ba ga karkatar da magana dõmin ya taimake ta.