Surat Sad, aya ta 33

38:33

رُدُّوهَا عَلَيَّۖ فَطَفِقَ مَسۡحَۢا بِٱلسُّوقِ وَٱلۡأَعۡنَاقِ ٣٣

Ruddūhā 'alayya fatafiqa mashā bis-sūqi wal-a'nāq

"Ku mayar da su a gare ni." Sai ya shiga yankansu1 da takõbi ga ƙwabrukansu da wuyõyinsu.

Bayanan ƙasa

1 Sulaimãna ya yanka dawãkin,dõmin kallonsu yã hana shi salla, wadda take farlu ainin ce a gare shi, amma tattalin kãyan yãƙi farlu kifãya ce. Anã gabãtar da farlu ainin a kan farlu kifãya. Wannan kuma ya nũna cewa anã cin dõki idan wani dalĩli bai hana ba. Dũbi Sũra ta 16, ãyã ta 8.