Innallaha wa mala'ikatahu

Fassara: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِيِّۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ صَلُّواْ عَلَيۡهِ وَسَلِّمُواْ تَسۡلِيمًا ٥٦

Innallāha wamalā'ikatahū yusallūna 'alan-nabiyyi yā'ayyuhal-ladhīna āmanū sallū 'alayhi wasallimū taslīmā

Lalle, Allah da malã'ikun Sa sunã salati1 ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Bayanan ƙasa

1 Salãtin Allah ga Annabi, shĩ ne ɗaukaka darajarsa a kõyaushe. Salãtin malã'iku, shĩne istigfãri da addu'a a gare shi. Salãtin mutãne, shĩ ne ibãda da istigfãri da addu'a a gare shi da tawassuli da shi dõmin neman Allah Ya karɓi ibãdarsu. Salãti sau ɗaya wãjibi ne a kan kõwane Musulmi a tsawon rayuwarsa, sa'an nan kuma sunna ce a cikin kõwace salla. Kuma mustahabbi ne a cikin kõwane mazauni da wurin ambatonsa.

Rubutun Latin taimako ne na karatu wanda Qabas ta rubuta daga Larabci. Ku koyi haruffan Larabci da tajwidi don furta kalmomi daidai.

Karanta Surat Al-Ahzab gaba ɗaya

Tambayoyi

Ina Innallaha wa mala'ikatahu take a cikin Alƙur'ani?

Innallaha wa mala'ikatahu tana cikin Surat Al-Ahzab, 33:56.