Surat Hud, aya ta 5

11:5

أَلَآ إِنَّهُمۡ يَثۡنُونَ صُدُورَهُمۡ لِيَسۡتَخۡفُواْ مِنۡهُۚ أَلَا حِينَ يَسۡتَغۡشُونَ ثِيَابَهُمۡ يَعۡلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعۡلِنُونَۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ ٥

Alā innahum yathnūna sudūrahum liyastakhfū minhu alā hīna yastaghshūna thiyābahum ya'lamu mā yusirrūna wamā yu'linūna innahū 'alīmu bidhātis-sudūr

To, lalle sũ sunã karkatar1 da ƙirjinsu dõmin su ɓõye daga gare shi. To, a lõkacin da suke lulluɓẽwa da tufãfinsu Yanã sanin abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanãwa. Lalle Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãzã.

Bayanan ƙasa

1 Bã su son su ga mai yi musu wa'azi, sabõda haka idan sun tsinkãyi Annabi daga nesa, sai su ɓũya, dõmin kada ya gan su, balle ma har ya yi musu wa'azi. Kuma har idan ya sãme su da wa'azinsa, sai su sanya tufãfinsu su rufe idanunsu da kunnuwansu kamar yadda mutãnen Nũhu suka yi masa a lõkacin da yake yi musu wa'azi. Ka dũba sũratu Nũh' sũra ta 71.