Surat Ghafir, aya ta 15

40:15

رَفِيعُ ٱلدَّرَجَٰتِ ذُو ٱلۡعَرۡشِ يُلۡقِي ٱلرُّوحَ مِنۡ أَمۡرِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦ لِيُنذِرَ يَوۡمَ ٱلتَّلَاقِ ١٥

Rafī'ud-darajāti dhul-'arshi yulqir-rūha min amrihī 'alā man yashā'u min 'ibādihī liyundhira yawmat-talāq

Mai ɗaukaka darajõji (dõmin mũminai), Mai Al'arshi, Yanã jẽfa rũhi 1daga al'amarinSa a kan wanda Ya so daga bãyinSa, dõmin ya yi gargaɗi kan rãnar gamuwa.

Bayanan ƙasa

1 Rũhi a nan, ga fahimta ta, Allah ne Mafi sani, shĩ ne karfin rai da basĩrar fahimtar addĩni da aiki wajen rãyar da shi, wanda Allah Yake sakãwa ga mãlamin da Yake nufin jaddada addini da shi a kan kõwane karni kamar yadda Hadisi ya zo da shi, ya kõre jidãlin mãsu jidãli.