Surat At-Tawbah, aya ta 98

9:98

وَمِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ مَن يَتَّخِذُ مَا يُنفِقُ مَغۡرَمٗا وَيَتَرَبَّصُ بِكُمُ ٱلدَّوَآئِرَۚ عَلَيۡهِمۡ دَآئِرَةُ ٱلسَّوۡءِۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ ٩٨

Waminal-a'rābi man yattakhidhu mā yunfiqu maghraman wayatarabbasu bikumud-dawā'ira 'alayhim dā'iratus-saw'i wallāhu samī'un 'alīm

Kuma daga ƙauyãwã akwai waɗanda1 suke riƙon abin da suke ciyarwa a kan tãra ce, kuma sunã saurãron aukuwar masĩfa a gare ku, aukuwar mummunar masĩfa ta tabbata a kansu. Kuma Allah ne Mai ji, Masani.

Bayanan ƙasa

1 Ƙauyãwã kashi biyu ne: Akwai wãwãye munãfukai mãsu ganin addĩni yã ɗõra musu nauyin biyan zakkã da sauran ayyukan alheri, sunã ɗaukar sa kamar tãra da biyan kakkarai. Kuma akwai ƙauyãwa mãsu hankali sun sani Annabi manzo ne daga Allah, sunã ɗaukar abin da addĩni ya azã musu duka ibãda ne, sunã fãtar kusanta da shi zuwa ga Allah, Ubangjinsu. To su mutãnen ƙwarai ne, zã su shigã Aljanna.