Surat Ash-Shu'ara, aya ta 221

26:221

هَلۡ أُنَبِّئُكُمۡ عَلَىٰ مَن تَنَزَّلُ ٱلشَّيَٰطِينُ ٢٢١

Hal unabbi'ukum 'alā man tanazzalush-shayātīn

Shin, (kunã so) in gaya1 muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka?

Bayanan ƙasa

1 Wannan dõmin raddi ne gamãsu cewa aljannu ke gayawa Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Alƙur'ãni. Aljannu bã su saukã sai ga maƙaryaci, mai zunubi' Muhammadu kuwa bã haka yake ba. Sabõda haka shi bã mahaukaci ba, kuma ba wanda aljannu suke gaya wa ba. Dukan abin da ya faɗa, to, wahayi ne daga Allah.