Surat An-Nur, aya ta 40

24:40

أَوۡ كَظُلُمَٰتٖ فِي بَحۡرٖ لُّجِّيّٖ يَغۡشَىٰهُ مَوۡجٞ مِّن فَوۡقِهِۦ مَوۡجٞ مِّن فَوۡقِهِۦ سَحَابٞۚ ظُلُمَٰتُۢ بَعۡضُهَا فَوۡقَ بَعۡضٍ إِذَآ أَخۡرَجَ يَدَهُۥ لَمۡ يَكَدۡ يَرَىٰهَاۗ وَمَن لَّمۡ يَجۡعَلِ ٱللَّهُ لَهُۥ نُورٗا فَمَا لَهُۥ مِن نُّورٍ ٤٠

Aw kazulumātin fī bahril lujjiyyin yaghshāhu mawjum min fawqihī mawjum min fawqihī sahābun zulumātu ba'duhā fawqa ba'din idhā akhraja yadahū lam yakad yarāhā wamal lam yaj'alillāhu lahū nūran famā lahū min nūr

Kõ kuwa kamar1 duffai a cikin tẽku mai zurfi, tãguwar ruwa tanã rufe da shi, daga bisansa akwai wata tãguwa, daga bisansa akwai wani girgije, duffai sãshensu a bisa sãshe, idan ya fitar da tãfinsa ba ya kusa ya gan shi. Kuma wanda Allah bai sanya masa haske ba, to, bã ya da wani haske.

Bayanan ƙasa

1 Ayyukan kafiri, wanda bã ya bin Hasken Allah ga aikinsa kamar mai ƙishirwa da wanda ya siffanta a sama yake, kõ kuwa kamar mai tafiya a cikin duffan da aka siffanta a wannan ãya.