Surat An-Nisa, aya ta 54

4:54

أَمۡ يَحۡسُدُونَ ٱلنَّاسَ عَلَىٰ مَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۖ فَقَدۡ ءَاتَيۡنَآ ءَالَ إِبۡرَٰهِيمَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَءَاتَيۡنَٰهُم مُّلۡكًا عَظِيمٗا ٥٤

Am yahsudūnan-nāsa 'alā mā ātāhumullāhu min fadlihī faqad ātaynā āla ibrāhīmal-kitāba wal-hikmata wa ātaynāhum mulkan 'azīmā

Ko suna hãsadar mutãne1 ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalar Sa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.

Bayanan ƙasa

1 Annabi Muhammadu, tsĩra da amincin Allah sun tabbata agare shi. An ce masa ɗan gidan Ibrahim domin Yahũdu su san shi ba kasasshe ba ne ga dangantaka, daga gare su. Kuma bai fita ba daga tsãrin cewa Annabãwa mãsu Littãfi a bãyan Ibrãhĩm, daga zuriyarsa za su fito. Kuma sun san wannan a cikin littãfinsu, watau Attaura.