ٱلرِّجَالُ قَوَّٰمُونَ عَلَى ٱلنِّسَآءِ بِمَا فَضَّلَ ٱللَّهُ بَعۡضَهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ وَبِمَآ أَنفَقُواْ مِنۡ أَمۡوَٰلِهِمۡۚ فَٱلصَّٰلِحَٰتُ قَٰنِتَٰتٌ حَٰفِظَٰتٞ لِّلۡغَيۡبِ بِمَا حَفِظَ ٱللَّهُۚ وَٱلَّٰتِي تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ وَٱهۡجُرُوهُنَّ فِي ٱلۡمَضَاجِعِ وَٱضۡرِبُوهُنَّۖ فَإِنۡ أَطَعۡنَكُمۡ فَلَا تَبۡغُواْ عَلَيۡهِنَّ سَبِيلًاۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيّٗا كَبِيرٗا ٣٤
Ar-rijālu qawwāmūna 'alan-nisā'i bimā faddalallāhu ba'dahum 'alā ba'din wabimā anfaqū min amwālihim fas-sālihātu qānitātun hāfizātul lil-ghaybi bimā hafizallāhu wallātī takhāfūna nushūzahunna fa'izūhunna wahjurūhunna fil-madāji'i wadribūhunna fa in ata'nakum falā tabghū 'alayhinna sabīlan innallāha kāna 'aliyyan kabīrā
Maza mãsu tsayuwa ne1 a kan mãtã, sabõda abin da Allah Ya fifita sãshensu da shi a kan sãshe kuma sabõda abin da suka ciyar daga dũkiyõyinsu. To, sãlihanmãtã mãsu ɗã'a ne, mãsu tsarẽwa ga gaibi sabõda abin da Allah Ya tsare. Kuma waɗanda kuke tsõron bijirewarsu, to, ku yi musu gargaɗi, kuma ku ƙaurace musu a cikin wurãren kwanciya, kuma ku dõke su. Sa'an nan kuma, idan sun yi muku ɗa'a, to, kada ku nẽmiwata hanya a kansu. Lalle ne Allah Yã kasance Maɗaukaki, Mai girma.
Bayanan ƙasa
1 Allah Ya sanya shugabancin gida da gudanar da tasarrufinsa a hannuwan maza domin ginar jikinsu, da hankalinsu da kuma dukiyarsu da suke ciyarwa ga sadãki da kuma nafaƙar (ciyarwar) gidan. Kuma Allah Ya aza wa mãta ɗa'a ga maza da kuma tsare farjojinsu domin kada su kawo wani baƙon da ba ɗan gida ba, a cikin gidan.