Surat An-Naml, aya ta 44

27:44

قِيلَ لَهَا ٱدۡخُلِي ٱلصَّرۡحَۖ فَلَمَّا رَأَتۡهُ حَسِبَتۡهُ لُجَّةٗ وَكَشَفَتۡ عَن سَاقَيۡهَاۚ قَالَ إِنَّهُۥ صَرۡحٞ مُّمَرَّدٞ مِّن قَوَارِيرَۗ قَالَتۡ رَبِّ إِنِّي ظَلَمۡتُ نَفۡسِي وَأَسۡلَمۡتُ مَعَ سُلَيۡمَٰنَ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ٤٤

Qīla lahadkhulis-sarha falammā ra'athu hasibathu lujjatan wakashafat 'an sāqayhā qāla innahū sarhum mumarradum min qawārīra qālat rabbi innī zalamtu nafsī wa aslamtu ma'a sulaymāna lillāhi rabbil-'ālamīn

Aka ce mata, "Ki shiga a gidan sarauta." To, a lõkacin da ta gan shi, ta yi zatona wai gurbi ne, kuma ta kuranye1 daga ƙwaurinta. Ya ce: "Lalle ne shi, gidan sarauta ne mai santsi daga madũbai." Ta ce: "Yã Ubangijĩna! Bã a rõƙon Allah sai da sunãyensa mãsu kyau, tis'in da taran nan, sai dai a dunƙule kamar a ce, "Inã rõƙon Allah da sunãyenSa da na sani da waɗanda ban sani ba." Lalle nĩ, na zãlunci kaina, kuma nã sallama al'amari tãre da Sulaiman ga Allah, Ubangijin halittu."

Bayanan ƙasa

1 Idan ĩmãni ya shiga a cikin zũciya, sai girman kai ya fita daga gare ta sarauniya Bilkisu tanã kuranye ƙafãfunta da niyyarta ta shiga a cikin ruwa dõmin ta nũna ɗã'arta ga umurnin Annabin Allah Sulaimãn kuma ta yarda da shiga gulbin da ba ta san tsawon zurfinsa ba, kõ da za ta mutu awurin ɗã'ã da taƙawa. Mace da sarauta iyakar girman kai ke nan, bãbu abin da zai gusar da shi sai ĩmãnin gaskiya.