وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّنۢ بُيُوتِكُمۡ سَكَنٗا وَجَعَلَ لَكُم مِّن جُلُودِ ٱلۡأَنۡعَٰمِ بُيُوتٗا تَسۡتَخِفُّونَهَا يَوۡمَ ظَعۡنِكُمۡ وَيَوۡمَ إِقَامَتِكُمۡ وَمِنۡ أَصۡوَافِهَا وَأَوۡبَارِهَا وَأَشۡعَارِهَآ أَثَٰثٗا وَمَتَٰعًا إِلَىٰ حِينٖ ٨٠
Wallāhu ja'ala lakum mim buyūtikum sakanan waja'ala lakum min julūdil-an'āmi buyūtan tastakhiffūnahā yawma za'nikum wayawma iqāmatikum wamin aswāfihā wa awbārihā wa ash'ārihā athāthan wamatā'an ilā hīn
Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbõbin ni'ima wasu gidãje kunã ɗaukar su da sauƙi a rãnar tafiyarku da rãnar zamanku, kuma daga sũfinsu1 da gãshinsu da gẽzarsu (Allah) Ya sanya muku kãyan ɗãki da na jin dãɗi zuwa ga wani lõƙaci.
Bayanan ƙasa
1 Sũfi, shi ne gãshin tumãki mai kama da audugã, wabar shi ne gãshin rãƙumi mai laushi, sha'ar, shi ne gãshin awaki da gezar dawãki. Bai ambaci audugã da kattãni ba, dõmin a wajen shũka suke.