لَيۡسَ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ جُنَاحٞ فِيمَا طَعِمُوٓاْ إِذَا مَا ٱتَّقَواْ وَّءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ ثُمَّ ٱتَّقَواْ وَّءَامَنُواْ ثُمَّ ٱتَّقَواْ وَّأَحۡسَنُواْۚ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ ٩٣
Laysa 'alal-ladhīna āmanū wa'amilus-sālihāti junāhun fīmā ta'imū idhā mat-taqaw wwa āmanū wa'amilus-sālihāti thummat-taqaw wwa āmanū thummat-taqaw wwa ahsanū wallāhu yuhibbul-muhsinīn
Bãbu laifi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin abin da suka ci, idan sun yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sa'an nan suka yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka yi taƙawa kuma suka kyautata1. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa.
Bayanan ƙasa
1 Yã maimaita faɗin taƙawa sau uku ga wanda ya tuba da shan giya da cãca dõmin ya nuna nauyinsu. Wanda ya shã giya kõ ya yi cãca, yã keta haddin Allah da alfarmar mutãne da darajar kansa. Sai yã yi taƙawa daga waɗannan zai iya rabuwa da su. Tsare su yanã cikin cika alkawari a tsakãnin mutum da Allah da kuma mutãne da ransa.