Surat Al-Ma'idah, aya ta 12

5:12

۞ وَلَقَدۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ وَبَعَثۡنَا مِنۡهُمُ ٱثۡنَيۡ عَشَرَ نَقِيبٗاۖ وَقَالَ ٱللَّهُ إِنِّي مَعَكُمۡۖ لَئِنۡ أَقَمۡتُمُ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَيۡتُمُ ٱلزَّكَوٰةَ وَءَامَنتُم بِرُسُلِي وَعَزَّرۡتُمُوهُمۡ وَأَقۡرَضۡتُمُ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗا لَّأُكَفِّرَنَّ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَلَأُدۡخِلَنَّكُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ فَمَن كَفَرَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ مِنكُمۡ فَقَدۡ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ ١٢

Walaqad akhadhallāhu mīthāqa banī isrā'īla waba'athnā minhumuthnay 'ashara naqīban waqālallāhu innī ma'akum la in aqamtumus-salawāta wa ātaytumuz-zakawāta wa āmantum birusulī wa'azzartumūhum wa aqradtumullāha qardan hasanal la ukaffiranna 'ankum sayyi'ātikum wala'udkhilannakum jannātin tajrī min tahtihal-anhāru faman kafara ba'da dhālika minkum faqad dalla sawā'as-sabīl

Kuma lalle Allah Yã riƙi alkawarin Banĩ lsrã' ĩla kuma Muka ayyana wakilai gõma shã biyu1 daga gare su kuma Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Inã tãre da ku, haƙĩƙa, idan kun tsayar da salla, kuma kun bãyar da zakka, kuma kun yi ĩmani da manzannĩ Na, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙĩƙa, Inã kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙĩƙa, Inã shigar da ku gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sanã gudãna a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kãfirta a bãyan wannan daga gare ku, to, lalle ne, yã ɓace daga tsakar hanya."

Bayanan ƙasa

1 An ayyana wakilai goma shabiyu daga ƙabĩlun Bani Isrãĩla goma sha biyu domin su ɗaukar musu alkawari daga wurin, kuma su tsare mutãnensu ga ganin ba a sãɓa wa alkawarin ba. An gina addinin Bani Isrãĩla a kan ƙabĩlanci. Saboda haka addininsu bã ya fita daga dã'irarsu.