Surat Al-Ma'idah, aya ta 117

5:117

مَا قُلۡتُ لَهُمۡ إِلَّا مَآ أَمَرۡتَنِي بِهِۦٓ أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبَّكُمۡۚ وَكُنتُ عَلَيۡهِمۡ شَهِيدٗا مَّا دُمۡتُ فِيهِمۡۖ فَلَمَّا تَوَفَّيۡتَنِي كُنتَ أَنتَ ٱلرَّقِيبَ عَلَيۡهِمۡۚ وَأَنتَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ ١١٧

Mā qultu lahum illā mā amartanī bihī ani'budullāha rabbī warabbakum wakuntu 'alayhim shahīdam mā dumtu fīhim falammā tawaffaytanī kunta antar-raqība 'alayhim wa anta 'alā kulli shay'in shahīd

"Ban faɗa musu ba fãce abin da Ka umurce ni da shi; watau: 'Ku bauta wa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku;' kuma nã kasance mai shaida a kansu matuƙar nã dawwama a cikinsu, sa'an nan a lõkacin da Ka karɓi raina1 Kã kasance Kai ne mai tsaro a kansu, kuma Kai, a kan dukkan kõme, Halartacce ne.

Bayanan ƙasa

1 Karɓar ran Ĩsã biyu ne, na duniya da na mutuwa.