وَكَذَٰلِكَ بَعَثۡنَٰهُمۡ لِيَتَسَآءَلُواْ بَيۡنَهُمۡۚ قَالَ قَآئِلٞ مِّنۡهُمۡ كَمۡ لَبِثۡتُمۡۖ قَالُواْ لَبِثۡنَا يَوۡمًا أَوۡ بَعۡضَ يَوۡمٖۚ قَالُواْ رَبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِمَا لَبِثۡتُمۡ فَٱبۡعَثُوٓاْ أَحَدَكُم بِوَرِقِكُمۡ هَٰذِهِۦٓ إِلَى ٱلۡمَدِينَةِ فَلۡيَنظُرۡ أَيُّهَآ أَزۡكَىٰ طَعَامٗا فَلۡيَأۡتِكُم بِرِزۡقٖ مِّنۡهُ وَلۡيَتَلَطَّفۡ وَلَا يُشۡعِرَنَّ بِكُمۡ أَحَدًا ١٩
Wakadhālika ba'athnāhum liyatasā'alū baynahum qāla qā'ilum minhum kam labithtum qālū labithnā yawman aw ba'da yawmin qālū rabbukum a'lamu bimā labithtum fab'athū ahadakum biwariqikum hādhihī ilal-madīnati falyanzur ayyuhā azkā ta'āman falya'tikum birizqim minhu walyatalattaf walā yush'iranna bikum ahadā
Kuma kamar wannan ne Muka tãyar da su, dõmin1 su tambayi jũna a tsakãninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Mẽne ne lõkacin da kuka zauna?" suka ce: "Mun zauna yini ɗaya ko sãshen yini." Suka ce: "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin2. Sai ya dũba wanne ne mafi tsarki ga abin dafãwa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum."
Bayanan ƙasa
1 Mahãwarar muminai a bãyan barcin shekara ɗari uku, amma duk da haka sunã cikin hankalinsu sunã mayar da al'amari ga Allah.
2 Birnin shi ne Tarasus. Sunan sarƙinsu Daƙayãnus.