Surat Al-Jathiyah, aya ta 16

45:16

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحُكۡمَ وَٱلنُّبُوَّةَ وَرَزَقۡنَٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَفَضَّلۡنَٰهُمۡ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ ١٦

Walaqad ātaynā banī isrā'īlal-kitāba wal-hukma wan-nubuwwata warazaqnāhum minat-tayyibāti wafaddalnāhum 'alal-'ālamīn

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai1 (wa Bãnĩ Isrã'ĩla Littãfi da hukunci da Annabci, Kuma Mun azurta su daga abũbuwa mãsudãɗi, Kuma Mun fĩfta su a kan mutãnen dũniya (a zãmaninsu).

Bayanan ƙasa

1 Bã Musulmi kawai aka aikowa Manzo ba,ba su kawai aka bã su sharĩ'a ba, kuma aka umurce su da binta ba, Banĩ Isrã'ĩla ma an bã su haka kuma sunɗaukaka a kan mutãne a lõkacin da suka yi aiki da sharĩ'ar, kuma suka ƙasƙanta a lõkacin da suka bar aiki da ita. Musulmi ma haka suke idan sun bar sharĩ'ar da Allah Ya aza su a kanta, zã su ƙasƙanta yadda Yahũdawa suka ƙasƙanta.