Surat Al-Isra, aya ta 55

17:55

وَرَبُّكَ أَعۡلَمُ بِمَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَلَقَدۡ فَضَّلۡنَا بَعۡضَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ عَلَىٰ بَعۡضٖۖ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا ٥٥

Warabbuka a'lamu biman fis-samāwāti wal-ardi walaqad faddalnā ba'dan-nabiyyina 'alā ba'din wa ātaynā dāwūda zabūrā

Kuma Ubangijinka ne Mafi sani game da wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun fĩfĩta sãshen Annabãwa a kan sãshe kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra.1

Bayanan ƙasa

1 Muƙãrana a tsakãnin Annabãwa. Allah Yã fĩfĩta waɗansu a kan waɗansu. Falalar Dãwũda a kan waɗansu Annabãwa da Zabũra ne to inã fĩfĩkon wanda aka bai wa Alƙur'ãni mafĩfĩcin littafi da sauran Annabãwa?.