۞ وَمِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ مَنۡ إِن تَأۡمَنۡهُ بِقِنطَارٖ يُؤَدِّهِۦٓ إِلَيۡكَ وَمِنۡهُم مَّنۡ إِن تَأۡمَنۡهُ بِدِينَارٖ لَّا يُؤَدِّهِۦٓ إِلَيۡكَ إِلَّا مَا دُمۡتَ عَلَيۡهِ قَآئِمٗاۗ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَالُواْ لَيۡسَ عَلَيۡنَا فِي ٱلۡأُمِّيِّـۧنَ سَبِيلٞ وَيَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ ٧٥
Wamin ahlil-kitābi man in ta'manhu biqintārin yu'addihī ilayka waminhum man in ta'manhu bidīnāril lā yu'addihī ilayka illā mā dumta 'alayhi qā'iman dhālika bi annahum qālū laysa 'alaynā fil-ummiyyina sabīlun wayaqūlūna 'alallāhil-kadhiba wahum ya'lamūn
Kuma daga Mutãnen Littãfi akwai wanda yake idan ka bã shi amãnar kinɗãri,1 zai bãyar da shi gare ka, kuma daga gare su akwai wanda idan ka bã shi amãnar dĩnari, bã zai bãyar da shi gare ka ba, fãce idan kã dawwama a kansa kanã tsaye. Wannan kuwa, dõmin lalle ne sũ sun ce, "Bãbu laifi a kanmu a cikin Ummiyyai.2" Suna faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa suna sane.
Bayanan ƙasa
1 Ƙinɗar Shi ne ũƙiyya dubũ gõma sha biyu, kuma ũƙiyya ɗaya tanã daidai da dirhami dubũ biyu da ɗari biyar kõ dĩnari dubu.
2 Bãbu laifi idan mun ci dũkiyarsu: Watau Bayahũde yana ganin cin dũkiyar wanda bã Bayahũde ba irinsa halal ne a gare shi.