وَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ قُتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمۡوَٰتَۢاۚ بَلۡ أَحۡيَآءٌ عِندَ رَبِّهِمۡ يُرۡزَقُونَ ١٦٩
Walā tahsabannal-ladhīna qutilū fī sabīlillāhi amwātā bal ahyā'un 'inda rabbihim yurzaqūn
Kada ka yi zaton waɗanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A'a, rãyayyu ne su, a wurin bangijinsu1. Ana ciyar da su.
Bayanan ƙasa
1 A cikin Hadisi an ruwaito cewa, Annabi yã ce Allah Yanã sanya rũhinsu a cikin cikkunan tsuntsãye mãsu kõren launi, sunã tafiya da su a cikin Aljanna sunã ci daga 'ya'yan itãcenta da rãna, sa'an nan su kõma zuwa ga wasu fitillu waɗanda aka rãtaye a cikin inuwar Al'arshi.