إِنَّ ٱللَّهَ يُدۡخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يُرِيدُ ١٤
Innallāha yudkhilul-ladhīna āmanū wa'amilus-sālihāti jannātin tajrī min tahtihal-anhāru innallāha yaf'alu mā yurīd
Lalle ne Allah Yanã shigar da waɗanda suka yi ĩmãni1 kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake nufi.
Bayanan ƙasa
1 Kashi na huɗu sũ ne mũminai waɗanda suke tsõron Allah, su tsaya a inda Yatsayar da su. Su ne mafi ƙarancin kashi ga uku na farko.